Gamayyar ƙungiyoyin gidan Arch Ɗangiwa sun ƙirayi masu ruwa da tsaki a Katsina da su yi koyi da abin da yake yi

Share this...
Share on Facebook
Facebook
0Tweet about this on Twitter
Twitter
Email this to someone
email

Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan Arch Ahmad Musa Dangiwa, shugaban bankin bada lamuni da gidaje na ƙasa wato “Federal Mortgage Bank” a taron da suka gudanar a ranar Lahadi sun jinjina masa.

Ƙungiyar ta ce dalilin ƙiran taro shine haɗa kan membobinta tare da yin aiki tuƙuru wurin wayar da kan al’umma kan irin aiyukan kishin ƙasa da uban tafiyan nasu ke yi a faɗin ƙasar nan.

Ta kuma ce ta yi taron ne domin jinjina wa Dangiwa bisa ayukkan alkhairin da yake yi dare da rana domin ci gaban jihar sa Katsina, Arewa da Najeriya baki ɗaya.

Ta bayyana Arch Ɗangiwa da gogaggen dan siyasa da ya bada gudunmwa a matakai daban-daban tun daga zamanin ANPP, CPC da kuma APC wanda kuma ta ce mutum ne mai son taimakon da kishin matasa da ya ciri tuta wurin koyar da yara da matasa maza da mata Sana’o’i tare da basu jari domin rage zaman banza.

A cewar jawabin da ƙungiyar ta fitar; “Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya kawo cigaba da dama a bankin bada lamuni da gidaje wato ‘Federal Mortgage Bank of Nigeria’ wanda ba’ataba samun wani da ya jagoranci bankin ya kawo ire-iren ci gaban da ya kawo tun bayan kafuwar bankin a shwkarar Alif 1973.

A cikin shekara ukku da watanni, Ɗangiwa ya kawo cigaban da ba’a taba samuba kama daga ginama ma’aikata gidaje bisa farashi mai rahusa, bada bashin gyaran gida ga ma’aikata wanda a wannan shekarar kaɗai Mortgage Bank ƙarƙashin jagorancin Arch Ahmed Musa Dangiwa ya bada “renovation loan na samada Biliyan 30” ga ma’aikatan kasar nan.

Baya ga waɗannan, ya kawo sabbin tsare tsare cikin har da maida harkokin bankin akan yanar gizo, sanya ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu cikin tsarin Mortgage Bank dadai sauransu

Mutumne wanda yashafe sama da shekara 30 amatsayin mai zaman kansa wanda dalilin haka yakasance kwararre akan aikinshi

Daga karshe kungiyar tayi ƙira ga masu ruwa da tsaki a jihar Katsina da su yi koyi da Dangiwa wurin kawo ci gaba a jihar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
0Tweet about this on Twitter
Twitter
Email this to someone
email

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *